Connect with us

News

Gidauniyar AMG Za Ta Tallafa Wa Marasa Lafiya Da Magani Kyauta

Published

on

IMG 20250731 WA0002

Shugaban Gidauniyar AMG, Dr Aminu Magashi Garba, ya ce kula da lafiyar al’umma, musamman marasa ƙarfi da masu fama da cututtuka, abu ne da ke da matuƙar muhimmanci a cigaban kowace ƙasa.

Dr Magashi ya bayyana hakan ne yayin wani taro da gidauniyar ta shirya a Kano tare da haɗin gwiwar Cibiyar Ma’aikatar Lafiya da Taimakon Gaggawa ta jihar.

Advertisement

Gudanar Da Dukkan Zaɓuka A Rana Ɗaya Abu Ne Wanda Zai Haifar Da Rudani —Jami’in INEC

Ya ce sun gudanar da taron ne domin tallafa wa marasa galihu ta hanyar rajistar su a asibitoci daban-daban da kuma samar musu da magunguna kyauta.

“Za mu kashe sama da naira miliyan biyu a wannan shekarar don cigaba da ayyukan kula da lafiyar mabukata a kananan hukumomi,” in ji Dr Magashi.

Advertisement

Ya ce gidauniyar na aiki tare da hukumomi da kungiyoyi masu zaman kansu wajen ganin an sauƙaƙa wa talakawa samun kulawar lafiya.

A nasa ɓangaren, Malam Salisu Umar Durumin Iya — kwararre a fannin sadarwa na Cibiyar Ma’aikatar Lafiya da Taimakon Gaggawa ta Kano — ya yaba da wannan mataki.

Advertisement

Ya ce akwai buƙatar masu hannu da shuni su riƙa taimaka wa marasa galihu da marayu domin rage wahalhalu da samun lada.

“Akwai kwamiti da gidauniyar ta kafa da zai gudanar da aikin zakulo mabukata da yi musu rijista domin samun kulawa kyauta,” in ji shi.

Advertisement

Daya daga cikin mahalarta taron, Alhaji Sha’ibu Ahmed Indabawa, ya yaba da kokarin gidauniyar.

Ya kuma roƙi sauran masu hali da su bada taimako domin rage matsalolin da ke addabar al’umma kamar mace-mace da barace-barace.

Advertisement

Taron dai ya samu halartar wakilai daga kungiyoyi daban-daban da ke aiki a fannin lafiya da taimakon jin kai.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending