News
Kamfanonin Sadarwa Za Su Ci Gaba Da Rajistar Layukan Waya — NIMC
Hukumar Kula da Shaidar ‘Yan Kasa ta Najeriya (NIMC) ta bayyana cewa kamfanonin sadarwa yanzu za su iya ci gaba da yin sabbin rajistar layukan waya (SIM), dawo da tsofaffi, da sauran sabis masu nasaba, bayan kammala nasarar canja tsarin tantance bayanan NIN zuwa sabon dandali na NINAuth.
Wannan mataki, a cewar hukumar, na nuna wani babban ci gaba wajen samar da ingantaccen tsarin da zai taimaka wajen tabbatar da sahihancin bayanan jama’a cikin tsaro da sauki.
Gidauniyar AMG Za Ta Tallafa Wa Marasa Lafiya Da Magani Kyauta
A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa dandalin NINAuth, wanda aka tsara kuma aka aiwatar da shi a karkashin kulawar NIMC, na bai wa kamfanonin sadarwa damar tantance NIN cikin sauri da sahihanci, lamarin da zai taimaka wajen dakile matsalolin da suka shafi sata ko amfani da bayanan bogi.
“A yanzu, kamfanonin sadarwa na da cikakken damar shiga dandalin domin gudanar da sabbin rajistar SIM, dawo da layin da aka rasa ko kuma sabunta bayanai,” in ji sanarwar.
NIMC ta bayyana cewa wannan tsarin wani bangare ne na kokarinta na tabbatar da cewa ana amfani da fasahar zamani wajen tantance bayanan ‘yan kasa, wanda hakan zai kara karfafa tsaron kasa da rage barna a harkokin sadarwa.
Sanarwar ta kuma kara da cewa ana sa ran sabon tsarin zai kawo sauki ga ‘yan kasa wajen samun sabis daga kamfanonin sadarwa ba tare da jinkiri ko tangarda ba.
-
News5 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News2 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
