Connect with us

News

Rugujewar Katanga Yayi Ajalin Uwa Da ‘Ya’yanta Biyar A Katsina

Published

on

images 6

Al’ummar garin Dankama da ke jihar Katsina sun shiga cikin makoki sakamakon mamakon ruwan sama da ya yi sanadin rugujewar katanga kuma ta afka kan yara biyar da mahaifiyarsu wadanda suka rasu nan take.

LEADSHIP HAUSA ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe biyu na safiyar ranar Litinin a gidan Muhammad Sani Garba Dankama, inda katanga ta murkushe su har lahira a cikin barcinsu.

Advertisement

Kotu Ta Yanke Wa ƴar India Hukuncin Zaman Gidan Yari Na Shekara 5 A Kano

An garzaya da wasu mutane uku da suka jikkata zuwa asibiti.

A cewar mahaifin marigayen, Dankama, ya bayyana cewa ba ya gida lokacin da katangar ta fado, inda ya ce ya kadu da jin labarin.

Advertisement

“Wannan lamarin ya faru da kusan mutane goma, amma mutane 6 sun riga mu gidan gaskiya. A yanzu haka, uku suna kwance a asibiti suna karbar magani,” kamar yadda ya shaida wa manema labarai.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending