News
Sojin Najeriya Sun Rusa Gidaje A Kaduna Duk Da Umarnin Kotun Jihar
Rundunar Sojin Najeriya ta sake rusa gidaje a Jaji, karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna, duk da umarnin kotu da ya haramta taɓa filayen da ake shari’a a kansu.
Kotun jihar Kaduna ƙarƙashin mai shari’a Justice Balogun ta bayar da umarnin hana rundunar sojin lalata ko wane gini a cikin shari’a mai lamba KDH/KAD/328/2018, wadda ta haɗa Alhaji Saminu Aminu da wasu mutane 266 da rundunar soji. Duk da haka, rahotanni sun tabbatar da cewa dakarun sojin sun mamaye yankin a daren Juma’a, inda suka rusa gidaje, makarantu.
Hukumomi Sun ƙayyade N20,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Sadaki A Kano
Wasu mazauna sun bayyana cewa sojojin sun zo cikin dare da manyan motoci da Hilux ɗauke da dakarun da suka yi rufa-rufa, tare da lalata gine-ginen jama’a ba tare da wani gargadi ba.
Bidiyon da aka samu ya nuna yadda mata da yara suke kuka da hawaye,
“An rusa mana makarantar allo, an rusa makarantar zamani, an rusa masallaci da gidajenmu gaba ɗaya. Mata da yara sun kwana a waje saboda babu inda za su shiga,” in ji wani mazaunin unguwar cikin damuwa.
Lauyan da ke kare al’ummomin da abin ya shafa, Dr. Kimi Livingstone Apah, ya bayyana matakin sojojin a matsayin take doka da rashin mutunta ikon kotu. Ya ce duk da cewa kotu ta bayar da umarnin hana rundunar sojin tabawa filin da ake shari’a kansa.
Ya bukaci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta dakatar da rundunar sojin daga irin wannan aiki, yana mai cewa abin da ke faruwa ya zama “kalubale ga doka, dimokuradiyya da mutuncin kotu.”
