Connect with us

News

‎Gwamnatin Legas Ta Kwace Baburan Okada 668 A Cikin Mako Guda.

Published

on

download (2)

Gwamnatin jihar Legas ta ce ta kwace Baburan Okada 668 a cikin sati guda saboda karya dokar hana zirga-zirgarsu a manyan hanyoyi, tare da kama mutum bakwai da ake zargi da yunkurin hana jami’ai gudanar da aikinsu.

‎Hukumar Lura da Muhalli da Laifuffuka ta jihar (Task Force) ce ta jagoranci wannan aikin, inda ta kai samame a wurare daban-daban da ake zargin masu Baburan Okada na haddasa matsalolin tsaro da hatsari ga jama’a.

Advertisement

Daga Sawaba Zuwa Asara: Baje Kolin Kasuwancin Siyasa A Kano

‎Shugaban hukumar, CSP Adetayo Akerele, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi ta bakin mai magana da yawun hukumar, Abdulraheem Gbadeyan.

‎Ya ce wannan mataki wani ɓangare ne na ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da doka kan haramcin zirga-zirgar babura a manyan hanyoyin da gwamnati ta ware.

Advertisement

‎A cewar sa, duk da gargadi sau da dama, masu babura na ci gaba da karya doka, abin da ya ce na jefa rayuka da dukiyar jama’a cikin barazana.‎

‎Shugaban hukumar ya jaddada cewa dukkan baburan da aka kwace za a gurfanar da su a kotu, sannan daga bisani a murƙushe su, bisa ga dokokin jihar.

Advertisement

 

 

Advertisement

DAILY POST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending