News
Wasu Manyan Mutane Ne Ke Daukar Nauyin Ta’addanci A Najeriya — Ƴansanda
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce akwai wasu fitattun mutane masu faɗa a ji a kasar da ke daukar nauyin ta’addanci da garkuwa da mutane ta hanyar haramtacciyar hakar ma’adinai.
Kwamishinan ‘yan sanda na babban birnin tarayya Abuja, Ajao Adewale, ya bayyana haka ne a wani taron wayar da kan ‘yan jarida kan illolin hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.
‘Yan Bindiga Sun Ƙona Mutane 20 Da Ransu, Bayan Ajalin Masallata Sama Da 30 A Katsina
Ya ce wannan matsala ta na jawo wa Najeriya gagarumar asarar kuɗaɗe da suka kai Naira tiriliyan 13.7, kwatankwacin dala biliyan 9 a kowace shekara.
“Haramtacciyar hakar ma’adinai ta zama babban kalubale ga tsaron Najeriya, kuma na daga cikin manyan hanyoyin da ke rura wutar ayyukan ta’addanci,” in ji shi.
Hukumar NEITI da ke sa ido kan harkar albarkatun ƙasa ta ce Najeriya na asarar kusan dala biliyan 9 a kowace shekara sakamakon fasaƙwairin zinare da sauran albarkatun ƙasa.
Hukumar ta kara da cewa wannan aiki na hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba na lalata muhalli, karya dokoki, hana masu zuba jari, da kuma bayar da tallafi ga ayyukan ta’addanci.
Rahotanni sun nuna cewa wasu manyan mutane a Najeriya ke da hannu kai tsaye wajen daukar nauyin wannan aiki, inda suke amfani da ‘yan kasashen waje wajen aiwatar da shi. Haka kuma ana amfani da ‘yan bindiga wajen kare ayyukan don kaucewa bincike ko hukunci.
Adewale ya bayyana jihohin Zamfara, Nasarawa, Kogi, Kaduna, Neja, Kwara, Osun da kuma wasu sassan Abuja a matsayin wuraren da ake yawan gudanar da wannan haramtacciyar hakar ma’adinai.
Ya ce daga shekarar 2023 zuwa 2024, rundunar ta kama mutum 72 da ake zargi da hannu a irin wadannan ayyuka, inda ya kara da cewa jami’an tsaro za su ci gaba da daukar matakai na musamman domin dakile wannan barazana.
