Connect with us

News

’Yan Sanda Sun Kama Mutane 10 Da Ake Zargi da Sayan Baburan Sata A Kano

Published

on

IMG 20250822 WA0000

Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta sanar da cafke wasu mutane 10 da ake zargin suna siyan baburan sata, bayan da aka kama wanda ake zargi na farko da satar baburan jama’a.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ranar Alhamis.

Advertisement

Wasu Manyan Mutane Ne Ke Daukar Nauyin Ta’addanci A Najeriya  — Ƴansanda 

Sanarwar ta bayyana cewa, a yayin bincike, jami’an tsaro sun gano karin babura guda bakwai da ake zargin an sace su, kuma daga baya aka mayar da su ga mamallakansu.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba da jajircewar jami’ansa wajen yaki da laifuka da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Advertisement

Ya kuma jaddada kudirin rundunar na ci gaba da gudanar da ayyuka na musamman domin murkushe masu aikata laifuka a fadin jihar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending