News
NASSI, Reshen Jihar Nasarawa Zata Yi Bikin Kaddamar Da Bada Tallafi A Ranar 16 Ga Satumba, 2025
DAGA JOHN D. WADA, a Latiya
An fara shirye-shirye don bikin bude shirin karfafawa na wata kungiyar inganta harkokin kananan sana’oi da masana’antu wato Nigerian Association of Small Scale Industrialists (NASSI) a turance reshen jihar Nasarawa, mai taken “Gina Ilmi, Samar da Ayyuka, Tabbatar da Makoma da Ci gaban Kasuwanci”.
Shugaban kungiyar a jihar, kwamaret Nidan Sambo Manasseh ya bayyana wa wakilin mu cewa shirin karfafawar za a gudanar da shi ne a ranar Talata, 16 ga Satumba na shekarar 2025 da aie ciki a Nurses House, dake gab da babban filin wasa na garin Lafiya (babban birnin jihar) da karfe 11 na safe.
Kungiyoyi 87 Sun Mayar Da Martani Kan Zarge-Zargen Cin Hanci A Gwamnatin Kano
Shirin acewar kwamaret Manasseh zai tallafa wa kimanin wadanda zasu amfana mahalarta 50 daga kowane karamar hukumar jihar.
Shuganan qungiyar a jihar ya kuma kara bayyana cewa wasu manyan mutane da ake tsammanin za su halarci taron sun hada da matar gwamnan jihar, Haj. Salifat Abdullahi Sule, kwamishinan wasanni da ci gaban matasa, hon. Kwanta Yakubu, shugaban ALGON, Hon. Safiyanu Isa Andaha da kwamishinan muhalli, Hon. Margaret Elayo.
Sauran sun hada da kwamishinan mata da ci gaban al’umma, misis Hauwa Samuel Judbo, D.G na cibiyar bunkasa al’umma, Haj. Habiba Balarebe Suleiman, kwamishinan kasuwanci, masana’antu da zuba jari, Hon. Mohammed Sani Otto da shi kansa, shugaban NASSI na jihar.
A lokacin shirin karfafawa da tallafin, za a kuma gabatar da dabarun samar da sabulu, sabulu mai ruwa, jelly, gwalgwal, bleach, turare, da kuma yin zane-zane da sauran sana’oin hannun dabandaban.
Binciken wakilin mu ya kuma gano cewa kawo yanzu dai a jihar ta Nasarawa din NASSI ta gina tsarin gine-ginen al’umma tareda tallafa musu a bangarorin sana’oin hannun dabandaban masu karfi a dukkan yankunan gudanarwa 13, tare da hade da manyan ‘yan kasuwa da masu kirkire-kirkire sama da 6,474 da ke aiki don tsara makomar tattalin arzikin jihar baki daya.
