News
Gwamnatin Shugaba Tinubu Ta Kusa Fara Cin Bashi Daga Opay Da Moniepoint —Dino Melaye
Tsohon ɗan takarar gwamnan Jihar Kogi, Sanata Dino Melaye, ya caccaki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan yadda ta ke ci gaba da neman basussuka daga ƙasashen waje da cibiyoyin kuɗi, yana mai cewa lamarin na iya kaiwa ga yin bashi daga kamfanonin hada-hadar kuɗi na intanet, irin su Opay da Moniepoint.
Dino ya yi wannan furuci ne a wata hira da tashar Arise Television a ranar Litinin, inda ya zargi gwamnatin da jefa al’ummar ƙasar cikin mawuyacin hali ta hanyar ci gaba da ciyo basussuka marasa amfani ga talakawa.
Dokar Ta Ɓaci A Ɓangaren Ilimi Tana Buƙaci Ɗaukar Matakin Gaggawa A Kano
Ya bayyana cewa, “Ana fama da matsananciyar yunwa a ƙasar nan. Me ya sa shugaban ƙasa zai nemi bashi na dala biliyan 1.7 daga Bankin Duniya? Me ya sa Majalisar Dattawa ta amince da bashin har na dala biliyan 21 zuwa yanzu, sannan akwai wasu kuma da ke tafe?”
Melaye ya ƙara da cewa “Wannan gwamnati ce mafi sakaci a tarihin Najeriya. Idan ana samun kuɗaɗen shiga, me ya sa kuma ake ci gaba da neman bashi? Ba abin mamaki ba idan nan gaba muka ga gwamnati ta koma neman bashi daga Opay da Moniepoint.”
