Connect with us

News

Gamayyar cibiyoyin mahaddata Alkur’ani ta karrama tsohon Gwamnan Kano Ganduje 

Published

on

IMG 20250926 WA0007

Gamayar Cibiyoyin Mahaddata Alƙur’ani ta Ƙasa ƙarƙashin jagorancin Gwani Yusuf Hamza Yusuf, Garkuwar Hafizai, ta sanar da al’ummar musulmi musamman mahaddatan Alƙur’ani Mai Girma cewa, wannan cibiyar ta bai wa tsohon Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje shaidar karramawa tare da naɗa shi muƙamin, Khadimul Huffazul Qur’an, duba da irin cigaban da yake bai wa ƙungiyoyin addinin Musulunci.

Ƙungiyar ta kafa hujja da irin yadda tsohon Gwamnan kuma tsohon shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, yake gina masallatai da makarantu da kuma babban aikin alherin da yake yi na musuluntar da Maguzawa, wanda ya shafe fiye da shekaru 20 yana yi, a ƙarƙashin Gidauniyarsa ta GANDUJE FOUNDATION.

Advertisement

Ba Kano ce ta fi kiwacce jiha cin jarabawar NECO a bana ba – Bincike

Sannan harwayau, ya shafe tsawon shekaru yana ba da kujerun Umra da Hajji, da kuma ba da tallafi ga malamai da basu ababen hawa, don sauƙaƙa musu ziyarce-ziyarce.

Ƙungiyar ta ce, wannan naɗi an yi shi ne bisa amincewar dukkan shugabannin rassan ƙungiyar na jihohi 36 haɗi da Abuja.

Advertisement

Kungiyar ta kuma yi Allah wadai da wasu mutane dake son saka siyasa a harkar addini, inda ta yi kira ga magoya bayan ta da su cigaba da biyayya da kuma addu’a ga shugabannin su, da zaman lafiyar ƙasa bakiɗaya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending