Connect with us

News

An Gudanar Da Taron Bada Shaidar Karatu Na Gidauniyar Marcelino A Jami’ar Isyaka Rabiu

Published

on

IMG 20250926 WA0012

DAGA SAFIYA MUHAMMAD USMAN

Gidauniyar Marcelino tare da hadin gwiwar Cibiyar Koyar da Sana’a ta Masu Bukata ta Musamman ta gudanar da taron bada shaidar kammala karatu ga dalibai da suka amfana da tallafin karatu, a wani gagarumin taro da aka shirya a Jami’ar Isyaka Rabiu da ke Kano.

Advertisement

Taron, wanda ya samu halartar manyan baki daga jami’o’i da cibiyoyi daban-daban, ya kasance wani mataki mai muhimmanci wajen karfafa ilimi da samar da damar dogaro da kai musamman ga masu bukata ta musamman a jihar.

Gamayyar cibiyoyin mahaddata Alkur’ani ta karrama tsohon Gwamnan Kano Ganduje 

A jawabinsa yayin taron, shugaban gidauniyar Dr. Marcelino Munoz, ya bayyana cewa wannan shiri na bada tallafin karatu yana daga cikin manyan manufofin gidauniyar na taimakawa matasa masu hazaka domin su samu damar kammala karatunsu cikin nasara.

Advertisement

Haka zalika, shugaban jami’ar ya jaddada cewa ilimi shi ne ginshikin ci gaban kowace al’umma, tare da yabawa shugabancin cibiyar koyar da sana’a ta masu bukata ta musamman bisa irin kokarin da suke yi wajen inganta rayuwar masu bukata ta musamman a Kano.

A nasa jawabin, shugaban cibiyar, Farfesa Rufa’i Yusuf Ahmed, ya bayyana cewa cibiyar ta kafa wannan shiri ne domin tallafawa masu bukata ta musamman ta hanyoyi daban-daban domin su samu damar dogaro da kansu. Ya kuma bayyana cewa hadin gwiwarsu da Gidauniyar Marcelino wani muhimmin mataki ne na inganta ilimi da wayar da kan al’umma a jihar.

Advertisement

Babban sakataren gidauniyar, Falalu Ali Alhassan, ya bayyana cewa shugaban gidauniyar ya yi tattaki tun daga kasar Mexico domin halartar wannan muhimmiyar rana, inda ya jinjina masa bisa daukar nauyin karatun daliban tun daga farko har zuwa lokacin kammala karatu ba tare da an karbi ko sisi daga gare su ba.

Shi ma mai kula da ayyukan gidauniyar a Najeriya, Hisbullah Abdullahi Bichi, ya bayyana farin cikinsa kan yadda aka gudanar da taron, inda ya ce fiye da dalibai 120 ne suka kammala karatun a karkashin shirin. Ya kuma yi kira ga al’ummar Kano da su yi amfani da wannan dama ta musamman, wacce ke bai wa dalibai damar karatu kyauta har zuwa matakin kammala karatunsu.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending