Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Kaddamar Da Sabon Tsarin Biyan Haraji Don Inganta Tattalin Arzikin Jihar 

Published

on

Hukumar Tattara Kudaden Shiga ta Jihar Kano (KIRS) ta gabatar da wani sabon tsari na zamani da nufin sauya yadda al’umma ke biyan haraji a fadin jihar, tare da tabbatar da inganci, gaskiya da sauƙi a tsarin tattara kudade.

Wannan sabon tsarin, wanda ke cikin manufofin gwamnatin Kano na ƙara yawan kudaden shiga na cikin gida da rage dogaro da tallafin gwamnatin tarayya, ya mai da hankali ne kan amfani da fasahar zamani da haɗa bayanan masu biyan haraji da Lambar Shaidar Dan Kasa (NIN).

Advertisement

Hukumar ta ce matakin zai taimaka wajen gano masu kauce wa biyan haraji da kuma hana maimaita rajista da sunaye daban-daban.

A cewar KIRS, sabon tsarin zai tilasta wa duk wanda yake da hakkin biyan haraji a jihar yin rajista ta amfani da NIN dinsa, tare da samar da sabbin hanyoyi masu sauƙi na biyan haraji ta yanar gizo, ta na’urorin POS ko kuma kai tsaye ta bankuna.

Advertisement

Babban Daraktan Sashen Tabbatar da Biyan Haraji da Tilastawa na hukumar, Muhammad Abba Aliyu, ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da KIRS ta shirya tare da haɗin gwiwar Kungiyar Tabbatar da Kyakkyawan Shugabanci (PACC).

“Wannan sabon tsari zai sauƙaƙa hanyoyin biyan haraji ga al’umma tare da tabbatar da tsafta da gaskiya a tsarin. Duk kudaden da aka tara za su shiga asusun gwamnatin jihar kai tsaye ba tare da sun ratsa hannun wasu jami’ai ko wasu asusu na daban ba,” in ji Aliyu.

Advertisement

Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su ba da haɗin kai wajen biyan haraji domin bai wa gwamnati damar gudanar da ayyukan raya kasa da inganta rayuwar jama’a.

Kano na neman zama sahun gaba

Advertisement

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa ɗaukar wannan mataki wani bangare ne na shirin ta na zama jiha ta farko wajen tattara haraji cikin sauƙi da inganci a Najeriya. Gwamnatin ta ce manufar hakan ita ce rage yawan mutanen da ke kauce wa biyan haraji da kuma magance korafe-korafen jama’a kan yadda ake karɓar kudaden haraji a hannun mutane ba tare da hujja ba.

Haka kuma, gwamnati ta ce sabon tsarin zai taimaka wajen gyara tsarin tattara kudade, samar da tsari mai gaskiya da sauƙi, da kuma ƙarfafa ci gaban jihar Kano ta hanyar samar da ayyukan more rayuwa da tabbatar da shugabanci nagari, wanda shi ne ɗaya daga cikin manyan manufofin gwamnatin Abba Kabir Yusuf.

Advertisement

Wakiliyarmu Kabiru Basiru Fulatan ya ruwaito cewa taron ya samu halartar kungiyoyin ‘yan kasuwa, ƙungiyoyi masu zaman kansu, manyan ƙungiyoyin ƙwararru, da kuma masu unguwanni daga sassa daban-daban na fadin jihar Kano, tare da ma’aikatan gwamnati.

Masu halartar taron sun yaba da wannan sabon tsarin, inda suka ce matakin zai taimaka wajen samar da tsarin haraji mai tsafta da sauƙi, tare da ƙara yarda tsakanin gwamnati da al’umma.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending