News
Farfesa Mahmood Yakubu Ya Sauka Daga Kujerar Shugaban Hukumar Zaɓe Ta INEC
Farfesa Mahmood Yakubu ya sauka daga kujerar Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).
Yakubu, wanda aka nada a shekarar 2015, ya yi wa’adin shekaru biyar sau biyu a ofis.
A ranar Talata, ya mika ragamar shugabanci ga May Agbamuche, kwamishina a hukumar, wacce za ta rike mukamin a matsayin mai rikon kwarya.
Tsohon shugaban hukumar ya roƙi tsofaffin abokan aikinsa da su ba wa mai rikon kwaryar cikakken hadin kai har zuwa lokacin da za a nada sabon shugaban hukuma na dindindin.
Ana sa ran Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai sanar da sabon shugaban hukumar zabe a kowanne lokaci daga yanzu.
Nadin sabon shugaban INEC na daga cikin muhimman batutuwan da ake sa ran za a tattauna a taron Council of State da aka shirya gudanarwa daga nan zuwa karshen mako.
-
News5 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News4 days ago
ICPC Ta Wanke Femi Gbajabiamila Daga Zargin Badakalar Hukumar Bogi
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Dakile Yunkurin Sace Jariri Da Wasu Ma’aikatan Asibiti A Jigawa
