Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Kaddamar Da Shirin Rigakafin Kyanda Ga Yara Sama Da Miliyan 7.8 A Jihar 

Published

on

Gwamnati za a fara yi wa mutane allurar rigakafin zazzabin cizon sauro

Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da sabon shirin rigakafin haɗin gwiwa na cutar kyanda da kyanda bi iska (Rubella), wanda ake ake sa ran fiye da miliyan 7 da dubu 800 (7.8m) a dukkan kananan hukumomi 44 na jihar.

An kaddamar da shirin ne a karamar hukumar Tofa a ranar Litinin, inda aka bayyana cewa za a gudanar da shi daga 6 zuwa 16 ga Oktoba, 2025, da nufin ƙarfafa rigakafi da kare lafiyar yara a fadin jihar.

Gwamnatin Kano Ta Kaddamar Da Sabon Tsarin Biyan Haraji Don Inganta Tattalin Arzikin Jihar 

Da yake jawabi yayin taron manema labarai a Cibiyar Kula da Lafiya  da ke Tofa, Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya ce wannan shiri wani gagarumin mataki ne da gwamnati ke ɗauka wajen tabbatar da lafiyar jama’a, musamman mata da kananan yara.

Ya bayyana cewa cutar Rubella — wadda ake kira German Measles — na da sauƙin kamuwa da ita a wajen yara, amma tana da barazana ga mata masu juna biyu, inda za ta iya haddasa matsaloli masu tsanani ga jarirai kamar bulewar zuciya, kurma ko matsalar gani.

Dakta Yusuf ya ƙara da cewa haɗa rigakafin kyanda da Rubella da kuma shirin rigakafin Polio da sauran rigakafi na yau da kullum, na nuna jajircewar gwamnatin Kano wajen samar da ingantaccen kiwon lafiya, tare da bin manufar Kungiyar Lafiya ta Duniya (WHO) ta kawar da cutar Rubella kafin shekarar 2030.

Kwamishinan ya yi kira ga iyaye da masu kula da yara da su tabbatar sun kai ’ya’yansu cibiyoyin lafiya don karɓar rigakafin. Ya jaddada cewa alluran kyauta ne kuma suna da matuƙar muhimmanci wajen kare lafiyar yara da tabbatar da ingantacciyar rayuwa.

Advertisement

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending