Connect with us

News

Ministan da PREMIUM TIMES ta bankado ya yaudari Najeriya da shaidun kammala karatu na Karya ya ajiye aiki

Published

on

1759865516024

Bayan bincike masu zurfi da PREMIUM TIMES ta gudanar da ya fallasa ministan Kimiyya, Nnnaji da tafka cuwacuwar takardun kammala karatunsa da na NYSC, a ranat Talata, ya mika takardar ajiye aikin sa ga shugaban Tinubu.

Kakain fadar shugaban Kasa, Bayo Onanuga ya tabbatar da karbar wannan takarda in da ya yi masa fatan alkhairi a a abinda ya sa a gaba,

Gwamnatin Kano Ta Kaddamar Da Shirin Rigakafin Kyanda Ga Yara Sama Da Miliyan 7.8 A Jihar 

PREMIUM TIMES, ta bi dalla-dalla yadda Nnnaji ya rika buga shaidun kammala karatyun sa na digiri daga jami’ar Najeriya UNN, da kuma sahidar kammala aikin yi wa kasa hidima, NYSC da duk na karya ne.

Da wadannan takardu ne aka tantance shi a majalisar dattawa tun a shekarar 2023.

Nnaji da kansa ya amsa laifin cewa tabbas ba jami’ar Najeriya ba ce ta bashi wannan shaidar kammala digiri, buga abinsa yayi a kasuwa ya cigaba da harkokinsa a mastsayin wanda ya kammala digiri.

Ita kanta jami’ar ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa Nnaji bai kammala karatunsa na Digiri ba, daga baya kaucewa yayi ya kama gabansa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending