Connect with us

News

‎Yadda Matar Wani Soja Ta Cinna Masa Wuta Ya Mutu ‎

Published

on

Unguwa gawa

Wani soja mai muƙamin Laftana a rundunar sojan Najeriya, Samson Haruna, ya mutu bayan da matarsa ta cinna masa wuta a lokacin da suka samu sabani a gida.

‎Lamarin mai cike da firgici da tausayawa ya faru ne a ranar 22 ga Satumba, 2025, a Wellington Bassey Barracks da ke Ibagwa, ƙaramar hukumar Abak, a jihar Akwa Ibom.

‎Ministan da PREMIUM TIMES ta bankado ya yaudari Najeriya da shaidun kammala karatu na Karya ya ajiye aiki

‎Rahotanni sun bayyana cewa matarsa, Mrs. Samson Haruna, ta watsa masa fetur sannan ta kunna masa ashana a lokacin da suke cikin zafafan maganganu a gida. Wannan ne ya haifar da mummunar ƙonewa a jikinsa gaba ɗaya.

‎Wata majiya ta tsaro ta shaida wa masani kan batutuwan tsaro a Najeriya, Zagazola Makama, wanda ya wallafa labarin a shafin sa na X (wanda ake kira Twitter a da), cewa marigayin wanda kuma likita ne a 6 Battalion Regimental Medical Office (RMO), an garzaya da shi asibiti bayan samun mummunar ƙonewa.

‎“An fara ba shi kulawar gaggawa a Military Reference Section (MRS) da ke cikin barikin, kafin daga bisani a tura shi zuwa University of Uyo Teaching Hospital don ƙarin jinya,” in ji majiyar.

‎Sai dai duk da ƙoƙarin da likitoci suka yi don ceto ransa, Laftana Haruna ya mutu sakamakon raunin ƙonewar da ya samu.

Advertisement

‎Hukumar tsaro ta tabbatar da cewa an kama matar, kuma tana hannun jami’an tsaro yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

‎

‎ PLATINUM POST NEWS

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending