Connect with us

News

Shugaba Tinubu ya sauke hafsoshin tsaro, ya maye gurbinsu da wasu

Published

on

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sauke Janar Christopher Musa daga mukaminsa na Babban Hafsan Tsaron Kasa, da sauran hafsoshin tsaro na kasa baki daya.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sunday Dare, Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, ya fitar a ranar Jumma’a.

Advertisement

Tirela Tayi Sanadiyar Mutuwar Mutum 10, Ciki Har Da Mai Juna Biyu

A cewar sanarwar, an nada Janar Olufemi Oluyede, wanda shi ne Shugaban Sojin Ƙasa, a matsayin Sabon Babban Hafsan Tsaron Ƙasa.

An kuma naɗa Manjo Janar W. Shaibu a matsayin Shugaban Sojin Ƙasa, Air Vice Marshal S.K. Aneke a matsayin Shugaban Rundunar Sojin Sama, da Rear Admiral I. Abbas a matsayin Shugaban Rundunar Sojin Ruwa.

Advertisement

Manjo Janar E.A.P. Undiendeye, wanda shi ne Shugaban Sashen Leken Asirin Tsaro (Defence Intelligence), zai ci gaba da rike mukaminsa.

Sanarwar ta bayyana cewa wannan sauyi na cikin shirin gwamnati na inganta tsaron a Najeriya.

Advertisement

Shugaba Tinubu, ya gode wa tsohon Babban Hafsan Tsaron ƙasa, Janar Christopher Musa, da sauran tsoffin hafsoshi bisa gudunmawa da jagorancin da suka yi.

Ya kuma bukaci sabbin hafsoshin da su nuna ƙwarewa, jajircewa, da haɗin kai domin inganta tsaro a Najeriya.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending