Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Wayar Da Kan Mata Masu Juna Biyu Kan Kula Da Lafiyar Jarirai Ta Hanyar Shayar Da Nono Zalla

Published

on

1002440317
Spread the love

Gwamnatin Jihar Kano ta shirya wani taron wayar da kai ga mata masu juna Biyu kan muhimmancin shayar da jarirai nono zalla na tsawon wata shida ba tare da haɗa ruwa ba.

Taron wanda aka gudanar a Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke cikin birnin Kano, ya samu halartar mata masu juna biyu fiye da dari uku.

Shugaba Tinubu ya sauke hafsoshin tsaro, ya maye gurbinsu da wasu

Kwamishinan yaɗa labarai cikin gida na jihar, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, shi ne ya jagoranci shirin, wanda aka gudanar karkashin kulawar Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Da yake jawabi a wajen taron, Waiya ya ce gwamnatin Kano ta mayar da hankali sosai kan lafiyar al’umma, musamman mata masu juna Biyu da jarirai, inda ta ke ɗaukar matakan tabbatar da samun ingantaccen kiwon lafiya a jihar.

Advertisement

Ya ce, “Gwamna Abba Kabir Yusuf na son ganin cewa mata masu juna Biyu suna samun kulawa yadda ya kamata, kuma bayan haihuwa a tabbatar da shayar da jarirai nono zalla na tsawon wata shida ba tare da ruwa ba. Domin nono yana ƙunshe da ruwa da sinadarai masu gina jiki da kariya ga jarirai.”

Waiya ya ƙara da cewa bincike ya tabbatar da cewa ruwan da ake ba jarirai kafin lokaci yana iya jawo musu cututtuka, wanda hakan ke haddasa matsalolin lafiya. Ya kuma ja hankalin iyaye da su rungumi wannan shiri domin kare lafiyar jarirai da kuma rage kashe kuɗi wajen siyan madarar waje.

A nasa jawabin, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, wanda Ɗan Kadan Kano, Dr Bashir Ibrahim Muhammad ya wakilta, ya yabawa gwamnatin Kano bisa jajircewar da take yi wajen inganta lafiyar al’umma.

Sarkin ya shawarci mata su rika cin abinci mai gina jiki tun kafin haihuwa, domin taimaka wa lafiyar jarirai tun kafin haihuwa da bayan haihuwar su. Haka kuma ya bukaci mata su kasance masu zuwa awo akai-akai domin kula da lafiyar su da ta jarirai.

Advertisement

Taron ya samu halartar wakilin Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, wakilin shugaban Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad, da manyan jami’an lafiya daga sassa daban-daban na jihar.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *