News
Gwamnatin Kano ta soke aikin tsaftar muhalli na gobe Asabar
Gwamnatin Jihar Kano ta soke aikin tsaftar muhalli na karshen wata da aka shirya gudanarwa a gobe, Asabar 25 ga Oktoba.
Advertisements
Advertisements
A cikin sanarwar da ta fitar, gwamnatin ta bayyana cewa an ɗage aikin ne saboda gudanar da bikin gargajiya na Hawan Kalankuwa, wanda ya haɗu da ranar aikin.
Advertisements
Ta ce an yanke wannan shawara ne domin girmama da kuma ba da muhimmanci ga al’adun gargajiya na Kano, waɗanda ke zama abin alfahari da ɗaukakar mutanen jihar.
Advertisements
Advertisements
Advertisements
