Connect with us

News

Tirela Tayi Sanadiyar Mutuwar Mutum 10, Ciki Har Da Mai Juna Biyu

Published

on

Trucks and car crash

Gwamnatin jihar Ondo ta ce ta fara bincike domin gano wanda ke da mallakar motar ɗaukar kaya da ta yi mummunan hatsari a yankin Akungba-Akoko, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum goma, ciki har da wata mata mai juna biyu.

Hatsarin ya faru ne a daren Laraba a kan titin Owo–Akungba–Ikare Akoko, a karamar hukumar Akoko ta Kudu-Maso-Yamma ta jihar, lokacin da wata babbar mota mai ɗauke da kaya ta kauce hanya, ta shiga cikin shaguna da gidaje, abin da ya jawo asarar rayuka da dukiya.

Advertisement

Wata Tsohuwa Mai Shekaru 82 ‎Ta Haɗiye Kwaɗi 8 Masu Rai

Kwamishinan Shari’a na jihar, wanda kuma shi ne Babban Lauyan  gwamnati, Mista Kayode Ajulo, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.

A cewarsa, gwamnati za ta tabbatar da cewa duka direban da kuma mai mallakar motar za su fuskanci shari’a da zarar an gano su.

Advertisement

Ajulo ya ce gwamnatin jihar ta damu matuƙa da yadda hatsarori ke ta ƙaruwa a manyan hanyoyi sakamakon gangancin direbobi masu tuƙa manyan motoci.

 

Advertisement

 

NAN

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending