News
Wata Tsohuwa Mai Shekaru 82 Ta Haɗiye Kwaɗi 8 Masu Rai
Wata tsohuwa ‘yar kasar China mai shekaru 82 ta fada cikin matsanancin hali bayan ta haɗiye kwaɗi takwas masu rai domin neman magani ga ciwon bayanta, kamar yadda jaridar Hangzhou Daily ta ruwaito.
Rahotanni sun bayyana cewa matar, mai suna Madam Zhang, ta yanke shawarar haɗiye kwaɗin ne bisa wata tsohuwar al’adar gargajiya da ake cewa tana taimakawa wajen rage ciwon baya.
Dakarun Soji Sun Yi Nasarar Kashe Ƴan Ta’adda Sama Da 50 a Borno Da Yobe
Danta ya bayyana cewa ta haɗiye kwaɗi uku a rana ta farko sannan ta ƙara biyar a rana ta biyu — tana fatan hakan zai warkar da ciwon bayan da ta dade tana fama da shi.
An ruwaito cewa ta umarci ’yan uwanta su kamo mata ƙananan kwaɗi — waɗanda ba su wuce girman tafin hannu ba — amma bata bayyana musu abin da za ta yi da su ba. Sai bayan ta fara jin zafi sosai a ciki ta amsa cewa ta haɗiye kwaɗin, lamarin da ya sa aka garzaya da ita zuwa asibitin Jami’ar Zhejiang da ke birnin Hangzhou.
Likitoci sun gano cewa Zhang ta kamu da cutar ƙwari mai suna Sparganum, wadda ta lalata wani ɓangare na hanjinta. Bayan makonni biyu na jinya da magani, an sallame ta daga asibiti.
-
Opinion7 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion6 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News5 days ago
Likitan El-Rufai Ya Shiga Matsala Kan Zargin Bayar Da Rahoton Jinya Na Bogi
