News
Matasa Biyar Sun Mutu A Hatsarin Kwale-kwale A Gombe
Akalla matasa biyar ne suka mutu a wani hatsarin Kwale-kwale da ya faru a kogin Nafada, da ke karamar hukumar Nafada a jihar Gombe.
Lamarin ya faru ne a ranar Asabar lokacin da jirgin ruwan da ke ɗaukar fasinjoji zuwa kasuwar wani kauye ya kife a tsakiyar hanya, inda dukkan matafiya suka fada cikin ruwa.
Wani Ɗalibin Jami’a Ya Kashe Abokinsa, Ya Binne Gawarsa A Bayan Gidansu
Wadanda suka mutu a hatsarin sun hada da Najib Ibrahim (18), Hauwa’u Jidda Adamu Siddi Dogal (15), Ummati Haruna Baraya (16), Umaira Gidado (16), da Amina Jaliya (15).
Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana jimaminsa kan faruwar lamarin, yana mai cewa abin ya matukar girgiza shi musamman ganin cewa matasa ‘yan ƙuruciya ne suka rasa rayukansu cikin wannan iftila’i.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Ismaila Uba Misilli, ya fitar, gwamnan ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan da al’ummar Nafada baki ɗaya, tare da rokon Allah Ya jikansu, Ya kuma ba iyalansu hakurin jure rashi.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
