Connect with us

News

‎Sojojin Amurka Sun Kammala Tsara Irin Farmakin Da Za Su Kawo Wa Najeriya  ‎

Published

on

images 5

Sojojin Amurka sun kammala tsara tsare-tsaren farmaki da za su iya kai wa Najeriya, bayan umurnin Shugaba Donald Trump na kare Kiristoci daga hare-haren ‘yan ta’adda, in ji rahoton jaridar The New York Times a ranar Alhamis.

‎Jami’an Amurka sun bayyana cewa, duk da wannan shirin, ba zai yiwu sojojin su kawo karshen rikicin tsawon shekaru a Najeriya ba. A cewar su, matakin farko zai kasance tallafawa jami’an tsaro na Najeriya wajen kai farmaki kan Boko Haram da ISWAP ta hanyar samar da bayanan sirri da kayan tallafi.

Advertisement

Jirgin Ƙasa Ya Murƙushe Direban Adaidaita Sahu Da Fasinjoji

‎Mataki na gaba kuma ya kunshi amfani da jiragen sama marasa matuki (drones) wajen kai hari kan sansanonin ‘yan ta’adda a arewacin Najeriya. Sai dai, shirin na fuskantar matsaloli sakamakon rufe wasu matattarar jiragen sama a Jamhuriyar Nijar.

‎Maj. Jan. Paul D. Eaton (mai ritaya) ya ce babban farmakin soja a Najeriya “zai zama koma-baya,” inda ya kara da cewa kai hare-hare da jiragen sama kaɗai ba zai kawo tasiri mai dorewa ba.

Advertisement

‎Shugaba Trump ya ce ya umarci Ma’aikatar Yaki ta shirya domin mataki mai yiwuwa, yana mai cewa “Addinin Kirista na fuskantar barazana” a Najeriya. Duk da haka, gwamnatin Najeriya ta musanta wannan kallon, inda Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa Najeriya “ta tsaya tsayin daka a matsayin dimokuradiyya mai bin doka da kare ‘yancin addini.”

‎Jami’an rundunar AFRICOM sun nuna cewa rikicin a arewacin Najeriya ya samo asali ne daga matsalolin kabilanci, addini da tattalin arziki, wanda ke sanya mafita ta soja kadai ba zai isa ba. Boko Haram da ISWAP sun kai hare-hare ga Kiristoci da Musulmi, suna amfani da rashin adalci a wasu yankuna domin fadada tasirinsu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending