News
Kotu Ta Yanke Wa Wani Ma’aikacin Jiyya Hukuncin Ɗaurin Rai Da Rai Saboda Kashe Marasa Lafiya 10 Da Gangan
Wata kotu a ƙasar Jamus a ranar Laraba ta samu wani ma’aikacin jinya da laifin kashe wasu marasa lafiya 10 a yayin da yake bakin aiki.
Kotun, wacce ke Aachen, ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai tare da ayyana cewa saboda girman laifinsa, ba zai samu yafiya ba har zai bayan shafe a ƙalla shekaru 15 a ɗaure.
An Kama Wani Mutum Kan Zargin Kashe Matarsa Mai Shekaru 15, A Sakkwato
Har zuwa yanzu dai ba a kai ga gama tantance adadin marasa lafiyar da ma’aikacin jinyyar mai shekaru 44 ya zama sanadin mutuwarsu ba.
A cewar lauya mai ƙara, mutane 13 sun mutu bayan ma’aikacin jinyar ya bai wa marasa lafiyar allurar bacci a yayin da yake aiki da wani asibiti da ke yammacin birnin Aachen a tsakanin watan Disambar 2023 zuwa Mayun 2024.
Tun da fari, ana tuhumarsa da laifuka 9 na kisan kai da yunƙurin kashe mutane 34. Sai dai a ƙarshen zaman shari’ar, kotun ta yanke wa wanda ake ƙarar hukuncin kashe mutane 10.
Sannan kotun ta same shi da laifin ƙoƙarin kashe mutane har karo 27.
Lauyoyi masu ƙara sun zargi ma’aikacin da bai wa marasa lafiya maganin bacci domin rage yawan aikinsa a lokacin da yake bakin aiki. Wanda ake zargin ya ce, ba ya ba su maganin ne domin kashe su ba.
Sai dai lauyoyinsa sun nemi da a wanke shi daga zargin.
Masu bincike sun cigaba da bankaɗo laifukansa na baya da ake zargin sa da su a Aachen wanda ke nuna akwai yuwuwar zai cigaba da fuskantar ƙarin tuhuma.
