Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Kafa Sabbin Jami’o’i, Polytechnic, NCE Na Tsawon Shekaru 7

Published

on

FB IMG 1762488671790

Gwamnatin tarayya ta amince da dakatar da kafa sabbin jami’o’i, kwalejojin kimiyya da na ilimi na tarayya na tsawon shekaru bakwai

Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) ta amince da dakatar da kafa sabbin jami’o’i, kwalejojin kimiyya (polytechnics), da kwalejojin ilimi na tarayya na tsawon shekaru bakwai a fadin ƙasar.

Advertisement

Shugabar Kasar Mexico Ta Fusata Bayan Wani Namiji Ya Rungumeta Ya Yi Yunkurin Sumbatarta A Bainar Jama’a

Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya sanar da haka a ranar Alhamis bayan taron majalisar da Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta.

A cewar ministan, matakin ya zama dole ne saboda damuwa da ake da ita kan rashin amfani da wasu cibiyoyin yadda ya kamata da karancin kayan aiki da kuma raguwa a ingancin ilimi a jami’o’in da ake da su yanzu.

Advertisement

“Wasu jami’o’in tarayya na aiki ne ƙasa da yadda ya dace, wasu ma ba su da ɗalibai fiye da 2,000,” in ji shi. “Wannan yana nufin asarar kuɗin gwamnati. Idan muna son inganta inganci kuma mu daina zama abin dariya a idon duniya, dole ne mu dakata da kafa sabbin jami’o’in tarayya.”

Alausa ya bayyana cewa dakatarwar ta shafi duka cibiyoyin gwamnati da masu zaman kansu. Sai dai ya ce an amince da sabbin jami’o’i tara masu zaman kansu da suka cika ƙa’idojin Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC).

Advertisement

Yayin da yake kwatanta wannan mataki da “sake farawa” ga tsarin ilimin Najeriya, ministan ya ce Shugaba Tinubu yana da cikakkiyar kishin ilimi kuma ya ba da umarni da a tabbatar da cewa kowane ɗan Najeriya yana samun ingantaccen ilimi mai daidaito da na kowace ƙasa a duniya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending