News
An Tsinci Gawar Tsohuwa Mai Shekara 96 A Ramin Bayan-gida Bayan Kwanaki Huɗu Da Ɓacewa A Kano
Hukumar kashe gobara a jihar Kano sun tabbatar da mutuwar wata tsohuwa ‘yar shekara 96, Habiba Ado, bayan da ta faɗa cikin ramin bayan-gida a ƙauyen Sarai, ƙaramar hukumar Dawakin Kudu.
Mai magana da yawun hukumar, ACFO Saminu Yusuf Abdullahi, ya bayyana cewa sun samu saƙon neman agaji ne da misalin 9:27 na safiyar ranar Alhamis, 6 ga Nuwamba, 2025, daga wani mazaunin yankin, Usman Adamu.
Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Kafa Sabbin Jami’o’i, Polytechnic, NCE Na Tsawon Shekaru 7
A cewar sanarwar, tawagar ceto ta isa wurin cikin gaggawa bisa umarnin daraktan hukumar, Alhaji Sani Anas, amma ta tarar da tsohuwar ta rigaya ta rasu.
Iyalanta sun sheda wa jami’ai cewa an shafe kwanaki huɗu ana neman ta, sannan kuma tana fama da larurar tabin hankali.
