News
Dakarun Soji Sun Kashe Ƴan Ta’adda Kusan 48 Cikin Kasa Da Sa’o’i 48 A Najeriya
Rundunar sojin Nijeriya ta ƙara zafafa ayyukan farautar ƴan ta’adda, masu tayar da ƙayar baya da kuma masu lalata tattalin arziki a sassan ƙasar, inda ta samu gagarumar nasara cikin sa’o’i 48 da suka gabata.
Wannan mataki na zuwa ne bisa umarnin babban hafsan sojin, Laftanar Janar Waidi Shaibu, wanda ya umarci dakarun da su tannatar da kakkaɓe ƴan ta’adda da ke sassan ƙasar.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na X, ta bayyana cewa sojoji sun kashe ƴan ta’adda bakwai, sun kama mutum 27 da ake zargi, tare da kwato makamai, harsasai da kuma man fetur da aka sace.
A yankin Arewa maso Gabas, dakarun Sector 3 na Operation Hadin Kai sun gudanar da aikin bincike da kame a ƙauyen Anguwan Church na ƙaramar hukumar Monguno a jihar Borno, inda aka cafke mutane 12 da ake zargin suna aiki a matsayin masu samar da bayanai ga ƴan ta’adda.
Haka kuma, dakarun Bataliya ta 192 sun yi wa mayaƙan ISWAP kwanton ɓauna a hanyar Gwoza zuwa Limankara, inda suka kashe uku daga cikinsu tare da ƙwace bindigar AK-47 da harsasai guda biyar.
A Damboa kuwa, dakarun Bataliya ta 25 sun kashe wani ɗan ta’adda da ya yi yunƙurin shiga sansanin su da sunan leƙen asiri.
A Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya kuwa, dakarun Operation Enduring Peace a jihar Kaduna sun kai samame a maboyar ƴan ta’adda a ƙaramar hukumar Kauru, inda suka kashe biyu daga cikin masu kai hare-hare kan fararen hula.
A jihar Filato ma dai haka abin yake, inda aka kama mutane huɗu da ake zargi da hannu a kisan mutane biyu a ƙaramar hukumar Riyom, yayin da a jihar Neja kuma, dakarun Operation Fansan Yamma suka kashe wani ɗan leƙen asirin ƴan ta’adda tare da ƙwace babur, wayar salula da wasu kayayyakin aiki.
