Connect with us

News

TALLAFIN GWAMNATI: Kashi 44 cikin 100 Ne Kaɗai Ke Isa Ga Masu Buƙata A Najeriya —Rahoto

Published

on

download 1

Bankin Duniya ya ce duk da kuɗaɗen da ake warewa a kai-a-kai domin tallafawa al’umma a Najeriya, kaso 44 cikin 100 kacal na tallafin ne ke kaiwa ga mutanen da aka tanada a taimaka musu.

A sabon rahoton da bankin ya wallafa a wannan mako, an bayyana cewa matsalolin da suka haɗa da tsarin tantance masu buƙata, ƙarancin kuɗi da kuma rabon da bai da tsari suke rage tasirin shirye-shiryen gwamnati.

Advertisement

An Kama Mutum 3 Kan Zargin Safarar Yara 17 A Zariya

Rahoton ya ce wadannan kura-kurai suna sa tallafin da ya kamata ya kasance kan talakawa, ya rika karkata zuwa hannun waɗanda ba su fiye buƙata ba, lamarin da ke barazana ga manufar rage talauci a ƙasar.

A kwanan nan Ministan Kuɗi, Wale Edun, ya ce gwamnati na cigaba da shirinta na tallafawa iyalai miliyan 15 ta hanyar biyan kuɗi ta yanar gizo.

Advertisement

Ya ce tuni iyalai miliyan 8.5 suka karɓi zagayen farko na biyan N25,000, yayinda sauran gidaje miliyan 6.5 ke jiran su karɓi nasu kafin ƙarshen shekara.

Fri Hausa ta ruwaito cewa masana a fannin tattalin arziki na ganin cewa sai an inganta tsarin tantance mabukata da kuma yadda ake rabon tallafi kafin gwamnati ta iya cimma manufarta ta inganta rayuwar miliyoyin ‘yan ƙasa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending