Connect with us

News

Wasu Batagari Sun Tone Ƙabari Tare Da Sace Gawar Cikinsa A Yobe

Published

on

Unguwa gawa

Rundunar ƴan sanda a jihar Yobe ta tabbatar da faruwar wani lamari da ya tayar da hankula, inda wasu da ba a san ko su wanene ba suka tono wani kabari tare da sace gawar da ke cikinsa a maƙabartar Makwalla.

Mai magana da yawun rundunar, ASP Dungus Abdulkarim, ya ce sun samu rahoton ne daga wani mutum mai suna Wakili Gambo, wanda ya sanar da cewa an bude kabari aka ɗauke gawar da ke cikinsa.

Advertisement

‎’Yan Bindiga Sun Yi Ajalin Jami’an Sa Kai 16 Tare Da Yin Garkuwa Da Mutane 42 A Neja ‎

A cewarsa, bayan samun bayanan, jami’an ƴan sanda sun isa wurin domin duba halin da ake ciki, sannan kuma an fara gudanar da bincike don gano wadanda suka aikata wannan mummunan aiki.

Kwamishinan ƴan sanda na jihar, CP Emmanuel Ado, ya yi Allah-wadai da lamarin, yana mai cewa rundunar ba za ta yi biris da duk wani da aka samu da hannu a ciki ba, domin doka za ta yi aikinta.

Advertisement

Ya kuma ja hankalin al’umma da su kafa kwamitocin kula da makabartu domin kare su daga irin wannan barna a nan gaba, tare da neman su riƙa sanar da jami’an tsaro duk wani abu da suka ga yana da take.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

MATASHIYA TV 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending