News
Gobara Ta Yi Ajalin Sama Da Mutum 80 Yayin Da Ke Ci Gaba Da Neman Mutane 250 Da Suka Bace
Hukumomin Hong Kong sun ce mutanen da suka mutu a gobara mafi muni da ta auku a birnin sun kai akalla mutane 83 yayin da ma’ikatan kwana-kwana ke ci gaba da neman mutane 250 da suka bace.
Har yanzu hayaki na tashi a dogayen benaye takwas na rukunin gidajen da gobarar ta auku.
Hukumomin sun ce an kaddamar da bincike kan musabbabin aukuwar gobarar mafi muni da ba a taba ganin irinta ba cikin shekaru 80 a birnin kasuwancin inda suka ce suna binciken gyaran da ake yi a gidajen inda aka bar wasu abubuwa kamar ledoji da shingen roba a wurin wadanda ke iya kamawa da wuta.
Yan sanda sun ce sun kama mutane uku bisa zargin sakaci na barin abubuwan da ke iya kamawa da wuta a wurin da gobarar ta tashi
Advertisements
