Connect with us

News

Fiye Da Musulmi 4,700 Suka Mutu A Rikice-rikicen Da Suka Auku A Filato — JCDA

Published

on

crisis scaled 1

Ƙungiyar Jasawa Community Development Association (JCDA) ta ce fiye da Musulmi 4,700 ne suka rasa rayukansu a rikice-rikicen da suka auku a Jihar Filato cikin shekaru 25 da suka gabata.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Yawale Muhammad ne, ya bayyana haka ne a taron manema labarai da aka yi a Masallacin Juma’a na Jos, yayin bukukuwan tunawa da wadanda suka mutu a rikice-rikicen da suka auku jihar.

Advertisement

Matashi Ya Hallaka Abokinsa Kan Yawan Tashinsa Sallar Asuba

A cewar JCDA, an tattara adadin mutanen da aka kashe ta hanyar bincike da rubuta takardun shaida na hare-haren da suka faru a sassa daban-daban na jihar.

Rikicin 2001 ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 700.

Advertisement

A 2002, a harin Eto Baba, daruruwan Musulmi ne aka kashe.

Rikicin Yelwa-Shendam na 2004 ya yi ajalin akalla mutane 700.

Advertisement

Rikice-rikicen bayan zabe na 2008 sun hallaka fiye da 1,000.

Hare-haren 2010 da suka shafi Dutse Uku, Gero da Kuru Jenta sun yi sanadin fiye da mutane 2,000.

Advertisement

A 2011, mutum 20 aka kashe a filin Idi na Rukuba Road.

A 2021, daruruwan matafiya Musulmi da ke kan hanyar dawowa daga gaisuwar  ga Sheikh Dahiru Bauchi sun rasa rayukansu a Rukuba Road.

Advertisement

A 2025, Musulmi 14 daga Zariya da ke kan hanyar zuwa bikin aure a Mangu aka kashe.

“Shugaban kungiyar ya ce:“28 ga Nuwamba rana ce da suka warewa domin tunawa da munanan  rikice-rikicen da suka taba faruwa a Matsayin Ranar jimami ce, ta addu’a da tunani.”

Advertisement

Ya kara da cewa ba nufinsu ba ne kawo tashin hankali, sai dai tabbatar da cewa gaskiya ta zauna a tarihi.

 

Advertisement

 

DAILY NIGERIAN

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending