News
Kotu Ta Sake Haramta Wa VIO Kama Masu Ababen Hawa
Kotun Daukaka Kara ta Abuja ta tabbatar da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke, wanda ya haramta wa Hukumar kula da lafiyar Ababen hawa (VIO) ikon dakatar da motocin jama’a, kwace su ko kuma kakaba tara.
Kotun ta kuma bada umarnin biyan N1 miliyan ga direban Abuja, Abubakar Marshal, wanda ya kai karar.
K-MAN Ta Taya Christopher Musa Murnar Rantsar da Shi a Matsayin Ministan Tsaro
A hukuncin da aka fara yanke wa a ranar 2 ga Oktoba, 2024, Mai Shari’a Nkeonye Evelyn Maha ta bayyana cewa babu wata doka da ke bai wa VIO ikon tilasta bin dokokin zirga-zirga.
Shari’ar ta samo asali ne daga korafin da lauyan kare hakin dan adam, Marshal, ya shigar, inda ya kalubalanci abin da ya kira cin zarafin ’yan Najeriya da VIO ke yi.
Kotun ta kuma bayyana cewa wannan hukunci bai shafi FRSC ba, wadda ita ce hukumar da doka ta amince da ita wajen aiwatar da dokokin zirga-zirga, tare da bayar da umarnin hana VIO ci gaba da tsoma baki ba bisa ka’ida ba.
