News
Mune Muka Bai Wa Amurka Bayanan Sirrin Maboyar ‘Yan Ta’addar Da Aka Kai Wa Hari —Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin Najeriya ta ce sai da ta amince tare da bayar da izini kafin gwamnatin Amurka ta ƙaddamar da harin bam a ƙasar.
Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar ne ya bayyana haka a zantawarsa da tashar Channels, inda ya ce Shugaban Najeriya Bola Tinubu yana sane da harin kafin a ƙaddamar.
Gwamantin Najeriya Ce Ta Bukaci Mu Kai Hari Kan ’Yan Ta’adda A Sakkwato – Amurka
Shugaban Amurka Donald Trump ne ya sanar da ƙaddamar da hari a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya, lamarin da ya ɗaga hankalin ƴan ƙasar.
Da yake jawabi kan harin a safiyar Juma’a, Tuggar ya ce, “yanzu da Amurka ta fara ba mu haɗin kai, za mu ci gaba da aikin ne a tare, kuma kamar yadda shugaban ƙasa ya nanata a jiya kafin ya amince da harin, dole aikin ya zama aikin haɗin gwiwa, kuma dole ya zama babu wani addini da ake hari,” in ji shi.
Ya ce Najeriya ƙasa ce mai addinai da dama, sannan ya ƙara da cewa gwamnatin Najeriya ba ta ce amince a mata karan-tsaye a kan ƴancinta ba.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
