News
Ba zaben 2027 ne ya dami Gwamnan Kano Abba Yusuf ba a yanzu – Waiya
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bai mayar da hankali kan batun zaɓen 2027 ba a halin yanzu, sai dai kan kokarin samar da ci gaba da inganta rayuwar al’ummar jihar.
Waiya ya bayyana hakan ne yayin wani taro da tsofaffin Ƙansilolin kananan hukumomi suka gudanar domin yin mubaya’a ga Shugaban Riƙon Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano, Hon. Abdullahi Zubairu Abiya.
A cewarsa, sau da dama a yayin zaman majalisar zartarwa, idan aka ambaci batun zaɓe mai zuwa, Gwamna Abba Kabir Yusuf kan jaddada cewa ba lokacin siyasa ba ne, face lokacin aiwatar da manufofin da za su amfani jama’ar Kano.
“Abin da ke gaban gwamnan Kano a yanzu shi ne cigaban jihar da walwalar ‘yan Kanawa. Zaben 2027 ba shi ne abin da ke damunsa ba,” in ji Waiya.
Ya kara da cewa gwamnatin jihar ta mayar da hankali ne kan muhimman bangarori kamar ilimi, kiwon lafiya da bunkasa rayuwar matasa, domin tabbatar da ci gaba mai dorewa.
Wannan bayani na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan yiwuwar hadakar jam’iyyun adawa gabanin babban zaɓen 2027 a Najeriya.
-
News2 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News6 days ago
Pantami Da Yaransa Sun Fantama Min Ƙarya, Domin Babu Inda Na Ba Shi Haƙuri, Inji Hajiya Naja’atu Muhammad
-
News4 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
