Connect with us

News

‎Gwamnatin Tarayya Ta Fito Da Sabbin Dabaru Domin Dakile Satar Amsa A Jarabawar WAEC Da NECO

Published

on

FB IMG 1762488671790

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar da wasu sabbin dabaru masu tsauri da nufin dakile satar amsa da sauran maguɗan jarabawa a WAEC da NECO, matakan da za su fara aiki daga shekarar 2026.

‎Ministan Ilimi, Dr. Maruf Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a Abuja tare da Karamar Ministar Ilimi, Farfesa Suwaiba Sai’d Ahmad, inda suka ce an ɗauki matakan ne domin maido da sahihanci, gaskiya da amincewar jama’a ga tsarin ilimi a Najeriya.

Advertisement

Kwankwaso Ya Taya Gwamnan Kano Abba Kabir Murnar Zagayowar Ranar Haihuwarsa

‎A cewar wata sanarwa da Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Boriowo Folasade, ta fitar, gyare-gyaren sun shafi dukkan matakan gudanar da jarabawar ƙasa, daga shirya tambayoyi zuwa tantance sakamako.

‎Sanarwar ta ce gwamnati za ta ƙarfafa amfani da fasahohin zamani, tare da tsaurara matakan kulawa, domin rage satar amsa da sauran laifukan da ke lalata martabar jarabawa.

Advertisement

‎Daga cikin manyan sauye-sauyen da aka sanar akwai sabon tsarin tsara tambayoyi, inda za a rika jujjuya jerin tambayoyi daga ɗalibi zuwa ɗalibi, duk da cewa tambayoyin iri ɗaya ne.

‎Ma’aikatar ta ce wannan dabara za ta rage damar haɗa baki a ɗakunan jarabawa, tare da tabbatar da cewa kowane ɗalibi na rubuta jarabawa ta musamman.

Advertisement

‎Haka kuma, Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada haramcin sauya makaranta a matakin SS3, tana mai cewa za a fara aiwatar da dokar cikin kwanaki masu zuwa, domin dakile sauye-sauyen makaranta na ƙarshe da ake zargin suna da alaƙa da satar jarabawa.

‎A wani mataki na ƙara inganta gaskiya da ɗaukar alhaki, an amince da sabbin ƙa’idojin kimanta ɗalibai na ci gaba (Continuous Assessment), inda aka tanadi lokutan miƙa bayanai kamar haka: Janairu (zango na farko), Afrilu (zango na biyu), da Agusta (zango na uku).

Advertisement

‎Sanarwar ta jaddada cewa dukkan hukumomin jarabawa — ciki har da WAEC, NECO, NBAIS da sauran su — wajibi ne su bi waɗannan ƙa’idoji, domin tabbatar da daidaito da ingancin bayanai a faɗin ƙasar.

‎Bugu da ƙari, ma’aikatar ta ce za a fara amfani da lambar shaidar ɗalibi ta musamman (Examination Learners’ Identity Number), wadda za ta bai wa gwamnati damar bibiyar ɗalibi a duk tsawon tsarin jarabawa.

Advertisement

‎A cewar jami’an ma’aikatar, wannan mataki zai taimaka wajen ƙarfafa sa ido, inganta tattara bayanai, da samar da ingantaccen tsarin tantancewa na dogon lokaci.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending