Connect with us

News

‎Akalla Yara 469 Ne Suka Mutu Sakamakon Fama Da Rashin Abinci Mai Gina Jiki A Kano ‎ ‎— Rahoto ‎

Published

on

Yaran da ke fama da yunwa da UNICEF ke kula da su a Sabuwar Marte a Jihar Borno
Spread the love

‎Akalla yara 469 ne suka mutu sakamakon Fama Da Rashin Abinci Mai Gina Jiki a tsakanin watan Janairu zuwa Yulin shekarar 2025 a Jihar Kano, kamar yadda wani rahoto ya bayyana.

‎Rahoton ya nuna cewa akalla kashi 57 na yaran da ke kasa da shekara biyar na fama da rashin girman jiki sakamakon illar da karancin abinci mai gina jiki ya musu.

Farashin Man Fetur Zai Iya Haura N1,400 Idan Nijeriya Ta Dogara Da Shigo Da Mai Daga Waje — Dangote

‎An bayyana hakan ne a wani taron wayar da kan manema labarai, inda Farfesa Ruqayya Aliyu Yusuf, malama a Jami’ar Bayero da ke Kano, ta gabatar da takarda mai taken “Understanding the Basics of Behavioural Change: Towards Improving Malnutrition in Kano State.”

‎Farfesa Ruqayya ta ce Rashin Abinci Mai Gina Jiki da rashin kyakkyawan tsarin abinci na ci gaba da zama manyan matsaloli a jihar, tana mai cewa Najeriya na daga cikin ƙasashen da ke da mummunan matsayi a Global Nutrition Index.

Advertisement

‎Ta bayyana cewa kimanin kashi 40 cikin 100 na yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar a Najeriya na fama da rashin girman jiki, yayin da rahoton UNICEF na shekarar 2025 ya nuna cewa Kano ta kai kashi 51.9 cikin 100, abin da ke nuna tsanantar matsalar a jihar.

‎A cewarta, “Talauci, ƙarancin wadatar abinci, rashin tsari wajen cin abinci, da ƙarancin wayar da kan jama’a kan kiwon lafiya su ne manyan dalilan da ke haddasa yawaitar Rashin Abinci Mai Gina Jiki.”

‎Haka kuma, Malam Amina Ado Yahaya, masaniyar harkokin noma, ta ce Jihar Kano ce ke da mafi yawan yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar masu ƙarancin nauyi a Najeriya, inda ta ce adadin ya kai kashi 42.6 cikin 100.

‎Ta ce halin da ake cikia na buƙatar ɗaukar matakan gaggawa, ciki har da ƙarfafa noman kayan lambu a gida-gida, domin inganta lafiyar iyalai a faɗin jihar.

Advertisement

‎Ta ƙara da cewa rashin sinadarin Vitamin A na daga cikin manyan dalilan da ke haddasa makanta ga yara, tare da ƙara tsananta cututtukan yara kamar kyanda.

 

DAILY TRUST 

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *