Connect with us

News

Kasafin  2026: Shugaba Tinubu, Shettima Da Mataimakansu Za Su Kashe Naira Biliyan 12.2 Wajen Tafiye-tafiye

Published

on

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, Mataimakinsa Kashim Shettima, tare da wasu manyan jami’an fadar shugaban ƙasa, na shirin kashe Naira biliyan 12.2 wajen tafiye-tafiye a cikin gida da kuma ƙasashen waje a shekarar 2026.

Wannan na cikin kasafin kuɗin fadar shugaban ƙasa da aka gabatar a gaban Majalisar Tarayya, wanda yanzu ke jiran amincewa.

Advertisement

Real Madrid ta naɗa Álvaro Arbeloa domin maye gurbin Alonso

Takardun kasafin sun nuna cewa fadar shugaban ƙasa na ci gaba da ba da fifiko ga hulɗa da ƙasashen waje, inda aka fi mayar da hankali kan tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje duk da matsin tattalin arziki.

An ware wa Shugaba Tinubu Naira biliyan 7.014 don tafiye-tafiye. Daga wannan, Naira biliyan 6.14 na nufin tafiye-tafiye na ƙasashen waje, yayin da Naira miliyan 873.89 aka tanade domin zirga-zirgar cikin gida.

Advertisement

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, zai samu Naira biliyan 1.732 don tafiye-tafiyensa. Daga cikin wannan, Naira biliyan 1.31 na nufin tafiye-tafiye na ƙasashen waje, yayin da Naira miliyan 417.49 aka ware don tafiye-tafiye cikin gida.

Bugu da ƙari, an ware Naira biliyan 3.433 domin tafiye-tafiye karkashin ofishin fadar shugaban ƙasa gaba ɗaya.

Advertisement

Haka kuma, kasafin ya tanadi Naira miliyan 179.01 domin sayen sabbin motoci ga shugaban ƙasa, yayin da Naira miliyan 375.19 aka ware don abinci da hidimar baƙi.

Wannan kasafin na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fuskantar hauhawar farashi da matsalolin tattalin arziki, lamarin da ke janyo muhawara a tsakanin al’umma kan yadda ake kashe kuɗaɗen gwamnati.

Advertisement

 

PUNCH

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending