News
Ƙungiyar Ma’aikatan Lafiya Ta JOHESU Ta Dakatar Da Yajin Aikin Bayan Kwana 84
Haɗakar JOHESU da ke ƙunshe da ƙungiyoyin ma’aikatan ɓangaren lafiya sun dakatar da yajin aikin da ta fara a fadin kasa bayan shafe kwanaki 84 ana gudanar da shi.
An dakatar da yajin aikin ne bayan wani taron gaggawa na fadada Majalissar Zartarwa ta Kasa (NEC) da aka gudanar a Abuja ranar Juma’a.
Gamayyar Kungiyar Ma’aikatan Lafiya JOHESU, Sun Janye Yajin Aikin Kwanaki 84 Da Suka Shafe Suna Yi
Rahotanni sun ce an kira taron ne domin duba sakamakon zaman sulhu tsakanin Gwamnatin Tarayya da JOHESU da aka yi ranar Alhamis a hedikwatar Ma’aikatar Kwadago da Aiki.
Gwamnatin tarayya ta kuma amince da janye umarnin “babu aiki, babu albashi”, tare da tabbatar da biyan albashin watan Janairu da kuma kare mambobin ƙungiyar daga hukunci.
Kungiyar ta umurci dukkan mambobinta da ke asibitocin tarayya da na jihohi da su koma aiki nan take.
Yajin aikin ya fara ne a 15 ga Nuwamba, 2025, kuma rahotanni sun ce ya yi mummunan tasiri ga harkokin kiwon lafiya a kasar.
