News
NAPTIP Ta Ceto Mata Bakwai Ake Zargin Ana Shirin Safarar Su Zuwa Ƙasar Iraki A Kano
Hukumar Hana Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP) ta ceto wasu mata bakwai da ake zargin ana shirin safarar su zuwa ƙasar Iraki, bayan samamen da jami’anta suka kai wani otel a unguwar Sabon Gari da ke jihar Kano.
Hukumar ta bayyana cewa samamen ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da rundunar shiyyar Kano ta samu, lamarin da ya kai ga kuɓutar da matan masu shekaru tsakanin 21 zuwa 24.
Mahara Sun Sace Shanu Sama Da 100 A Borno
Jami’in hulɗa da jama’a na NAPTIP a Kano, Mohammed Habib, ya ce jami’an hukumar sun kai farmakin ne a ranar Alhamis, inda suka kuma kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a safarar.
Ya ƙara da cewa binciken farko ya nuna an ɗauko matan ne daga kudancin Najeriya, inda aka yi amfani da Kano a matsayin wurin wucewa kafin a tura su zuwa Baghdad, babban birnin ƙasar Iraki, domin tilasta musu aiki.
A cewar hukumar, matan sun bayyana cewa wata mace da ake zargi a matsayin jagorar safarar ce ta shirya tafiyarsu, tare da haɗin gwiwar wani namiji da ya tsere, wanda jami’ai ke ci gaba da nema.
Tsarin tafiyar ya haɗa da sharadin cewa za su biya duk kuɗaɗen da aka kashe a kansu, tare da riba, bayan sun isa ƙasar da za su yi aiki.
Hukumar ta ce matan da aka ceto na hannunta a Kano, inda ake ba su kulawa, shawarwari da kuma taimakon farfaɗowa.
NAPTIP ta kuma bayyana cewa da zarar bincike ya kammala, za a gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu.
Hukumar ta sake jaddada kudurinta na rushe hanyoyin safarar mutane tare da kira ga al’umma su kasance masu lura da kuma kai rahoton duk wani abu da ke nuna alamun safarar mutane.
