News
’Yan Rakiyar Amarya 14 Sun Mutu Sakamakon Kifewar Wani Jirgin Ruwa A Kebbi
Aƙalla mutane 14 ne suka rasa rayukansu sakamakon kifewar wani jirgin ruwa a kogin River Niger da ke yankin Gumbi, cikin karamar hukumar Yauri dake jihar Kebbi , a arewa maso yammacin Najeriya.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mutanen da hatsarin ya rutsa da su na cikin tawagar da ke rakiyar wata amarya zuwa gidan mijinta a Gwarzo, cikin karamar hukumar Ngaski , lokacin da jirgin ruwan ya kife.
Malam Sulaiman Marafa Ya Karɓi Aiki A Matsayin Manajan Filin Jirgin Sama Na FAAN A Gombe
Shugaban karamar hukumar Yauri, Abubakar Shu’aibu, ya bayyana cewa sama da mutane 100 ne ke cikin jirgin a lokacin da lamarin ya faru.
Ya ce zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 14, ciki har da mata 13 da kuma karamin yaro guda.
A cewarsa, an riga an binne dukkan mamatan bisa ka’idojin addinin Musulunci.
Gwamnan jihar, Nasir Idris, ya aike da sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu da al’ummar masarautar Yauri, yana mai kira gare su da su karbi wannan ibtila’i a matsayin kaddara.
-
Opinion4 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News2 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
