News
Gwamnatin Jihar Kano Ta Kai Tallafi Ga Wadanda Gobara Ta Shafa a Garin Zago
Gwamnatin Jihar Kano ta ƙarƙashin Ma’aikatar Jin Кai da Rage Talauci ta kai tallafi ga al’ummar da gobara ta shafa a garin Zago da ke Кaramar Hukumar Ɗanbatta.
Tallafin na kuɗaɗe da aka yi jiya a garin na Zago da ke ƙaramar hukumar Ɗanbatta ya kai jimillar Naira miliyan shida da dubu ɗari biyar da saba’in da shida da ɗari biyar da talatin da bakwai da ɗigo talatin da uku (N6,576,537.33) an raba shi ga iyalai 28 da gobarar ta shafa a watan Fabrairu na shekarar 2025 da ta gabata.
Kamfanin Maltina Ya Ƙaddamar da Shirin Bunƙasa Noman Sha’ir a Jigawa, Manoma 20,000 Za Su Amfana
Da take jawabi yayin rabon tallafin, Babbar Sakatariyar ma’aikatar, Hajiya Amina Yusuf ‘Yargaya, ta ce gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf tana matuƙar damuwa da duk wata matsala da ta shafi rayuwar al’umma, musamman waɗanda suka fuskanci bala’i.
Ta tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa al’umma a duk lokacin da irin wannan ƙalubale ya taso domin tabbatar da jin daɗi da walwalar jama’a, tana mai kira ga waɗanda suka amfana da su yi amfani da abin da suka samu ta hanyar da ta dace.
Shi ma da yake jawabi, Sakataren Zartarwa na Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Kano (SEMA), Abdullahi Isyaku Kubarachi ya bayyana cewa an gudanar da binciken tantance girman asarar da gobarar ta afku kafin a samar sa tallafin.
Ya roƙi mutane da su rinƙa kashe wuta bayan gama aikin gida musamman da dare kafin su kwanta, yana mai tabbatar da cewa SEMA za ta ci gaba da aiki tare da sauran masu ruwa da tsaki domin taimakawa al’umma a duk lokacin da bala’i ya auku.
Haka zalika, Mashawarcin Gwamna na Musamman kan Ayyukan Jin Ƙai Dakta Garba Ibrahim ya buƙaci al’umma da su rinƙa yin taka-tsantsan don kaucewa afkuwar gobara, yana mai jaddada ƙudirin gwamnati na ci gaba da taimakawa duk wanda bala’i ya shafa.
A nasa ɓangaren, Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Kano kan Tallafin Al’umma, Muttaƙa Sani Gaya ya tabbatar da shirin gwamnatin Kano na ci-gaba da kula da walwalar al’umma, musamman masu rauni da waɗanda bala’i ya shafa.
Da yake bayyana farin cikinsa da tallafin, shugaban ƙaramar hukumar Ɗanbatta, Jamilu Abubakar Ɗanbatta wanda Abdulƙadir Muhammad ya wakilta, ya gode wa gwamna Abba Kabir Yusuf, yana mai cewa ba shakka taimakon zai taimaki waɗanda abin ya shafa wajen rage musu dukiyar da suka yi asara.
Waɗanda suka amfana da tallafin sun nuna godiyarsu ga gwamnatin Kano bisa tallafin da aka kawo musu a lokacin da suka fi buƙata.
