Connect with us

News

Matasa Biyu Sun Rasu Yayin Tserewa Masu Kwacen Waya A Kano

Published

on

FB IMG 1773145829094

Wasu matasa biyu ‘yan uwan juna, Sadiq Isyaku da Auwalu Isyaku, sun rasa rayukansu bayan sun nutse a wani kudiddifi da ke unguwar Kureken Sani a jihar Kano, yayin da suke ƙoƙarin tserewa daga wasu da ake zargin ƴan ƙwacen waya ne.

Jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

“Siyasar Da Ba Ta Da Adawa Ba Dimokuraɗiyya Ba Ce” — Comrade Salisu Gambo Ditol Ya Soki Yawaitar Sauya Sheƙar ‘Yan Siyasa

A cewarsa, lamarin ya faru ne a ranar Juma’a bayan da hukumar ta samu kiran gaggawa daga wani Muhammad Abba, wanda ya sanar da cewa wasu matasa biyu sun fada cikin ruwa.

Abdullahi ya bayyana cewa nan take jami’an hukumar suka garzaya zuwa wurin domin ceto su. Sai dai bayan an fito da su daga ruwan, an same su ba sa motsi.

“An garzaya da su asibiti, inda likitoci suka tabbatar da rasuwar su,” in ji shi.

Advertisement

Ya kara da cewa bayan kammala matakan da suka dace, an mika gawarwakin matasan ga mahaifinsu a unguwar Unguwa Uku domin yi musu jana’iza.

A cewar jami’in, binciken farko da hukumar ta gudanar ya nuna cewa matasan sun fada cikin ruwan ne yayin da suke ƙoƙarin tserewa daga wasu da ake zargin ƴan ƙwacen waya ne da suka bi su domin kwace musu wayoyi.

Lamarin ya jawo alhini a tsakanin mazauna yankin, inda ake kira ga hukumomi su ƙara ɗaukar matakan tsaro domin dakile ayyukan ƴan daba da masu aikata laifi a cikin al’umma.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending