News
Yan sandan Kano sun bindige masu satar mutane 3, sun ceto wasu mutane
Daga kabiru basiru fulatan
Jami’an ‘yan sanda a Kano sun yi nasarar bindige wasu masu garkuwa da mutane a kalla uku tare da ceto wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su a hannunsu.
Kakakin rundunar ‘yan sandanjihar, SP Abdullahi Haruna wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Kano a ranar Lahadi, ya ce an kashe masu garkuwar ne a wani artabu da ya barke tsakanin masu garkuwa da mutanen da jami’an tsaro.
SP Haruna ya ce an kubutar da wadanda aka sace ba tare da jin rauni ba, kuma tuni aka mika su ga iyalansu.
A cewarsa, “A ranar Asabar da misalin karfe 01;30 na dare ne aka samu rahoton cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun afka wa wani kauyen Katsina inda suka sace wani Elisha Aminu a karamar hukumar Tudun Wada a jihar Kano, suka yi garkuwa da ‘ya’yansa mata guda biyu: Zainab. Elisha, mai shekara 18, Nafisa Elisha mai shekara 16 kuma an kai su gaɓar dajin Falgore.
“Bayan samun rahoton kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya umurci tawagar ‘Operation Puff Adder’ jagorancin SP Kabir Aminu, jami’in ‘yan sanda na shiyya ta Tudun Wada da kuma jami’an tsaro daga rundunar ‘yan sandan da ke yaki da masu garkuwa da mutane a karkashin SP Shehu Dahiru domin ceto wadanda aka kashe tare da kamo masu laifin.
Jam’ian a lokaci guda suka fara aiki tare da taimakon wani rukunin ‘yan banga na gida mai suna “Yan Bula”.
An zagye dajin kuma ‘yan bindigar sun makale, sakamakon haka, an kwashe kimanin sa’o’i 2 ana gwabza artabu da su.
“An halaka uku daga cikin masu satar mutane, sannan an ceto mutanen biyu ba tare da sun jigata ba.
Amma wasu fusatattun mutane kuma sun kona daya daga cikin masu garkuwa da mutane.
“An mika gawawwakin zuwa babban asibitin Tudun Wada inda likita ya tabbatar da mutuwarsu.
An sake mika wadanda aka ceto zuwa iyalansu, sannan tura ƙarin jami’an Puff Adder zuwa dajin don ƙarin kame.
“Kwamishanan ‘yan sandan ya jinjinawa jami’an da suka shiga aikin kuma ya yaba da kokarin ’yan banga (‘Yan Bula) bisa goyon baya da taimakon da suke yi.”
Dajin Falgore dai yana nema ya zama wata matattarar masu satar mutane, duba da yadda rahotannin ayyukan masu satar mutane yake daɗa ƙamari a dajin.
Ko a shekarar da ta gabata, sai da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya sheda wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, cewa gwamnatin jihar Kano tana hadin gwiwa da sauran jihohi maƙota wajen yaƙar matsalolin na tsaro da yake faruwa a yankin na Dajin Falgore.
