Connect with us

News

Mutane 4 Sun Mutu, 53 Sun Jikkata A Sakamakon Hatsarin Mota A Kano ‎

Published

on

Akalla Mutane 21 Ne Suka Rasa Rayukansu A Wani Hatsarin Mota Da Ya Afku A Hanyar Kaduna Zuwa Abuja 

Hukumar kiyaye afkuwar haddura ta kasa FRSC reshen jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane hudu tare da jikkata wasu 53 a wasu hadarra daban-daban a Jihar.

Mai magana da yawun hukumar Abdullahi Labaran ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.

Advertisement

Masarautar Hadejia: Tarihin Shekaru Dari na Turjiyar Hadejia ya Mamayar Yan Mulkin Mallaka — 1906-2026 ‎ ‎

A cewar sanarwar hadari na farko ya faru ne a ranar Juma’a, 17 ga watan Afrilun da mu ke ciki, da misalin karfe 10:20 na dare a kan hanyar Bypass kusa da gadar Muhammadu Buhari da ke Hotoro a Kano.

Advertisement

Ya ce hadarin ya faru ne da wata tirela mai dauke da dabbobi da kayayyaki da kuma fasinjoji, inda motar ta taso daga Kasuwar Wudil ta Jihar Kano, tare da nufar Asaba a Jihar Delta a lokacin da lamarin ya faru.

Hukumar ta bayyana ce a binciken farko da ta gudanar ya nuna cewa direban motar ya gaza sarrafata sakamakon gudun da ya ke yi, a lokacin da ya ke tunkarar gadar saman, lamarin da ya kai ga faruwar hatsarin.

Advertisement

Sanarwar ta ce manya maza 59 ne hadarin ya rutsa da su daga ciki, 33 sun samu raunuka daban-daban, inda a ka ceto 24 ba tare da jikkata ba, ya yin da mutane biyu su ka rasa rayukansu.

Sanarwar ta ce, an kwashe wadanda su ka jikkata zuwa asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano domin kula da lafiyarsu, ya yin da ake ci gaba da kokarin kula da wuraren da hadarin ya afku tare da tabbatar da zirga-zirgar ababen hawa yadda ya kamata.

Advertisement

Labaran ya ce hatsarin na biyu ya hada da wasu motoci guda biyu da su ka hada da tirelar cike da dabbobi da kayayyaki da kuma fasinjoji, wadda ta taso daga Kasuwar Wudil, inda ta ke kan hanyar zuwa jihar Legas a ranar Asabar.

Labaran ya ce shi ma direban na biyu gudun wuce sa’a ne ya sanya ya yi karo da wata motar.

Advertisement

Ya ce fasinjoji maza 30 ne hadarin ya shafa, daga ciki 20 sun samu raunuka daban-daban, takwas an ceto su ba tare da jikkata ba, ya yin da mutane biyu su ka rasa rayukansu.

Acewarsa an kai wadanda su ka jikkata zuwa babban asibitin Wudil domin kula da lafiyarsu.

Advertisement

Kwamandan hukumar Idris Mohammed Lawal, ya bayyana takaicinsa kan yadda wasu direbobi ke saba ka’idojin hanya, musamman yadda su ke jigilar fasinjoji a tireloli da aka tanadar don daukar kayayyaki da dabbobi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending