Connect with us

News

Dakarun Soji Sun Kashe Mayakan ISWAP Da Dama A Yankin Tafkin Chadi

Published

on

‎Burkina Faso ta saki sojojin Najeriya Da Take Rike Da Su Na Tsawon Kwanaki 10

Dakarun Rundunar Operation HADIN KAI sun kai jerin farmaki na musamman ta sama, inda suka kashe mayakan ISWAP fiye da 30 tare da tarwatsa hanyoyin samun kayayyakinsu a ɓangaren jihar Borno na yankin Tafkin Chadi.

A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanal Kanal Sani Uba, ya fitar a ranar 22 ga Afrilu, ya bayyana cewa hare-haren sun gudana ne a daren 21 zuwa 22 ga Afrilu a yankin tsibirin Kaniram da ke Arewacin jihar Borno.

Advertisement

Gwamnatin Kano Ta Kammala Shirye-Shiryen Yin Auren Zawarawa 1500

Yadda Aka Gudanar Da Samamen

Advertisement

Bayan samun ƙwararan bayanan sirri da sa ido ta sama, rundunar ta tabbatar da taruwar kwale-kwalen ’yanta’adda fiye da 30 waɗanda ake amfani da su wajen safarar makamai da abinci.

Bayan tantance wuraren da kyau, jiragen yaƙin rundunar sun saki bama-bamai waɗanda suka tarwatsa kwale-kwalen tare da kashe aƙalla mayaƙa 30 a nan-take.

Advertisement

Rahotanni sun nuna cewa sauran mayakan da suka tsira sun runtuma cikin daji cikin halin ruɗani bayan rugujewar tsarin ba da umarninsu.

Latata Motocin Yaƙi a Sambisa

Advertisement

Haka kuma, rundunar ta kai wani samamen na daban a yankin Sowolwolo da ke cikin dajin Sambisa. A wannan hari, sojojin sun samu nasarar lalata motocin yaƙi guda uku maƙare da makamai da kashe ƙarin mayaƙa da dama da ke kusa da motocin.

Binciken bayan hari ya tabbatar da cewa ’yan ta’addan sun tafi da gawarwakin mambobinsu zuwa yankin Mallam Fatori domin yi musu jana’izar gaba-daya, wanda hakan ke nuna yawan asarar rai da suka yi.

Advertisement

Sanarwar ta ce a halin yanzu, dakarun kasa suna ci gaba da kewayen yankunan domin tabbatar da cewa mayakan da suka tsere ba su sake haduwa ba.

Babban kwamandan rundunar ya jinjina wa sojojin bisa wannan gagarumar nasara, inda ya bukace su da su ci gaba da matsa lamba har sai an kakkabe sauran ’yan ta’addan baki daya.

Advertisement

 

TRT AFRIKA 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending