Connect with us

News

Trump Ya Umarci A Harbe Duk Jirgin Ruwan Iran Ɗin Da Aka Gani A Hormuz

Published

on

Donald trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya ba da umarnin cewa a harbe duk wani jirgin ruwan Iran da aka kama yana dasa nakiya a mashigar ruwa ta Hormuz.

Wannan sanarwa ta fito ne, biyo bayan karuwar taƙaddama kan tekun da ke yankin Gabas ta Tsakiya.

Advertisement

Dakarun Soji Sun Kashe Mayakan ISWAP Da Dama A Yankin Tafkin Chadi

Trump ya bayyana cewa an bayar da wannan umarni ne don kare zirga-zirgar jiragen ruwa bayan zargin cewa Iran tana dasa nakiya a cikin ruwa don kawo cikas ga sufurin mai zuwa kasuwar duniya

Advertisement

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, shugaban na Amurka ya jaddada cewa kada a yi jinkiri wajen harbe duk wani jirgin ruwan Iran din da aka samu yana aikin dasa nakiya.

Baya ga umarnin harbin, ya kuma sanar da cewa Amurka ta ninka ayyukanta na kakkaɓe nakiya a mashigar ta Hormuz, abin da ya bata nasarar zaƙulo waɗanada aka dasa a ƙarƙashin ruwa har sau uku.

Advertisement

Wannan umarni ya zo ne sa’o’i kaɗan bayan rahotannin da ke cewa Iran ta kama wasu jiragen ruwan kasuwanci tare da harbin wasu, duk da cewa an tsawaita yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta a baya-bayan nan.

Hukumomin Iran sun bayyana wannan mataki na Amurka a matsayin haramtaccen fashi na teku a yankunansu.

Advertisement

 

RFI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending