News
Ƴan Bindiga Sun Ƙone Gidan Dagaci A Zamfara
Wasu ‘yan ta’adda a ƙarƙashin jagorancin Mai Rasha sun ƙone gidan wani basarake a garin Yankuzo, Babangida Hamza, a ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara a ranar Talata.
‘Yan ta’addan sun kuma ƙone shaguna da kwashe kayan abinci da sauran kayayyaki.
Kashi 70% Na Laifuka A Kano Na Da Alaƙa Da Miyagun Ƙwayoyi —Rahoton
Shugaban ƙauyen, Hamza, ya shaida wa DCL Hausa, a ranar Talata cewa ‘yan ta’adda suun shigo garin ne da safe da har zuwa kusan ƙarfe 03:30 na yamma.
“‘Yan ta’addan sun shiga garin suna harbe-harbe tare da wucewa garin basaraken inda suka ƙone fadar tasa,” in ji Kogon Yankuzo.
“Ina garin Tsafe a lokacin da na samu kira cewa an kai wa mutanena hari. Kawo zuwa 4:05 na yamma. Ban samu wani bayani game da mutane nawa aka kashe ko aka raunata ba. Sai dai an kwashe iyalaina daga gidan,” ya bayyana.
Basaraken ya ce an fasa shaguna da dama waɗanda yan bindigar suka sace kayan abinci a cikinsu.
Hamza ya ce, “An sanar mana da safe cewa sojoji sun kutsa wurin ‘yan bindiga wanda bai da nisa daga garinmu.”
“Bayan awanni kaɗan, sai ga ‘yan bindigar sun zo ɗaukar fansa garinmu. Kodayause suna farmakina, don haka, na yanke shawarar komawa shalkwatar ƙaramar hukumar inda nake gudanar da ayyukana,” ya faɗa.
Basaraken ya ce watanni shida da suke wuce ‘yan bindiga su sace shi a lokacin da suka yi zargin yana bai wa jami’an tsaro bayanai kan motsin ‘yan ta’adda a yankin. Daga baya suka sake shi.
Harin da aka kai wa Yankuzo na zuwa ne bayan kwanaki uku da an sace dakaci a garin Kaura Namoda, Ibrahim Dan Auta, Sarkin Yamman Kaura a gidansa.
A jihohin Zamfara, Katsina da Sakkwato, sarakuna na cikin mutane masu daraja da ‘yan ta’adda suke kai wa farmani a tsawon waɗannan shekaru.
Mai magana da yawun ‘yan sanda, Yazid Abubakar, bai amsa saƙon kar-ta-kwana da muƙa tura masa ba haka ma saƙonni ta WhatsApp kan harin da aka kai.
Ba mu kuma same shi ta waya ba a lokacin da muka kira shi.
