News
Tankar Mai Ta Murkushe Adaidaita Sahu
Mutum guda ya rasa ransa bayan wata tankar mai dauke da fetur ta murkushe wani Adaidaita Sahu da ke tsaye a yankin Oke Ado da ke birnin Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.
Rahotanni daga shaidun gani da ido sun ce hatsarin ya faru ne lokacin da wata tankar mai dauke da fetur ta kasa sarrafa kanta yayin da direbanta ke kokarin kauce wa wata mota da ke gabansa.
Tankar Mai Ta Murkushe Adaidaita Sahu
Tankar ta tsallaka zuwa dayan bangaren hanya inda ta murkushe wani Adaidaita Sahu da ke tsaye.
An bayyana cewa direban Adaidaita Sahu din ya mutu nan take sakamakon hatsarin.
A halin yanzu, jami’an hukumar kashe gobara ta Jihar Oyo sun isa wurin domin daukar matakan kariya, musamman don dakile yiwuwar tashin gobara sakamakon man fetur da ke cikin tankar.
