News
‘Yan Majalisar Wakilai 17 Sun Fice Daga Jam’iyyar ADC Zuwa NDC
Akalla ‘yan majalisar wakilai 17 sun sauya sheƙa daga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) zuwa Nigerian Democratic Congress (NDC), a wani sabon salo na sauye-sauyen siyasa da ke ƙara ƙamari gabanin babban zaɓen 2027.
An sanar da sauyin ne a zauren majalisar a ranar Talata yayin zaman majalisa, inda aka karanta wasiƙun ficewar ‘yan majalisar, lamarin da ke nuni da girgizar da ake samu a tsakanin jam’iyyun adawa.
Yau Tsohon Shugaban Kasa Marigayi Umaru Musa Yar’Adua Ya Cika Shekaru 16 Da Rasuwa
Wannan mataki na zuwa ne bayan wasu manyan jiga-jigan siyasa sun riga sun fice daga ADC zuwa NDC a farkon makon nan, matakin da ke ƙara ƙarfafa sabon tsarin haɗakar siyasa a ƙasar.
A wani ɓangaren kuma, ɗan majalisa Leke Abejide ya sauya sheƙa daga ADC zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), abin da ke nuna yadda yanayin siyasa ke sauyawa cikin sauri.
Daga cikin ‘yan majalisar da suka koma NDC akwai Yusuf Datti, Uchenna Okonkwo, Adamu Wakili, Thaddeus Attah, George Ozodinobi, Lilian Orogbu, Oluwaseyi Sowunmi, Peter Aniekwe, Mukhtar Zakari, George Oluwande da Munachim Umezuruike.
Sauran sun haɗa da Emeka Idu, Jesse Onuakalusi, Ifeanyi Uzokwe, Afam Ogene da Abdulhakeem Ado.Cikakken labari na nan tafe…
