Connect with us

Politics

Dr. Mohammed Musa Zango Ya Mayar Da Fom Din Takararsa Ga Uwar Jam’iyyar APC A Hukumance

Published

on

IMG 20260508 104834 435

Dan takarar kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya a karkashin jam’iyyar APC, Dr. Mohammed Musa Zango, ya mayar da fom din tsayawa takara da na nuna sha’awa ga uwar jam’iyyar APC a hukumance, tare da bayyana kwarin gwiwar samun nasara a zaben fidda gwani da kuma babban zaben 2027.

Dr. Zango, wanda shi ne wanda ya assasa gidauniyar Fatah Zango Foundation, ya gudanar da aikin mayar da fom din ne a dakin taro na Ladi Kwali Hall da ke Abuja Continental Hotel, wurin da jam’iyyar ta ware domin karbar fom din ‘yan takara.

Advertisement

Dakarun Sojin Sun Ceto Yaran Da Aka Sace Daga Gidan Marayu

Lamarin ya biyo bayan ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya da ya yi a ranar Lahadi 3 ga watan Mayun 2026.

Advertisement

A cikin sanarwar da ya fitar, Dr. Zango ya bayyana cewa zuwa lokacin da ya mayar da fom din nasa, shi ne kadai dan takarar da ya kammala tare da gabatar da dukkan takardun da ake bukata ga jam’iyyar.

Ya kuma gode wa magoya baya da masu ruwa da tsaki bisa goyon bayan da suke ci gaba da ba shi, yana mai bayyana cewa yana da yakinin samun nasara da taimakon Allah.

Advertisement

“Da karfin Allah da ikonSa za mu kai ga gaci,” in ji shi.

Dr. Zango ya jaddada aniyarsa ta samar da ingantaccen wakilci da kuma kawo ci gaba mai amfani ga al’ummar Kano ta Tsakiya idan aka ba shi dama.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending